Labarai
Mun taba bincikar Tinubu kan zargin safarar miyagun kwayoyi- FBI

Hukumar Bincike ta kasar Amurka FBI, ta tabbatar da cewa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kasance cikin mutanen da ta gudanar da bincike a kansu bisa laifukan safarar miyagun ƙwayoyi a farkon shekarun 1990.
Wannan na cikin wata takardar rantsuwa da hukumar ta gabatar wa wata kotun tarayya a birnin Washington DC, a matsayin wani ɓangare na ƙarar neman bayanan binciken shugaba Tinubu.
Sai dai hukuncin kotun bai tabbatar da cewa shugaba Tinubu ya aikata laifin safarar ƙwayoyi ko kuma an taɓa samun hukuncin laifi a kansa ba.
Hukumar FBI ta ce, wasu bayanan har yanzu ba za ta bayyana su ba saboda dalilan kare sirri da kuma hanyoyin binciken jami’an tsaro.
A nasa martanin, mai bai wa Shugaba Tinubu shawara kan harkokin yaɗa labarai, Sunday Dare, ya yi watsi da batun, ya na zargin cewa ana amfani da tsoffin bayanan Amurka ne domin siyasa gabanin zaɓen 2027 da ke tafe.
You must be logged in to post a comment Login