ilimi
Tinubu ya gargadi shugabannin jami’o’i
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya gargadi mahukuntan jami’o’in gwamnati da su guji kara kudin makaranta ba bisa ka’ida ba.
Shugaban ya bayyana hakan ne yayin da ya ke jawabi a garin Uyo yayin taron kammala karatu na jami’ar Uyo ta jihar Akwa Ibom da yammacin Alhamis din makon nan.
Tinubu wanda ya samu wakilcin karamin ministan ilimi, Dakta Yusuf Sununu, ya ce matakin na hana samun damar zuwa manyan makarantu, musamman ga matasa marasa galihu a kasar.
Haka kuma, ya kara da cewa, ƙarin kudin makaranta ba bisa ka’ida ba na yin illa ga ci gaba da bunkasar makarantun gaba da sakandare.
You must be logged in to post a comment Login