Labarai
Tinubu ya karɓi bakuncin sabon Shugaban Jamhuriyar Benin, Wadagni

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya karɓi sabon shugaban kasar Benin Romuald Wadagni, a gidansa da ke Ikoyi a birnin Legas ranar Litinin.
A cewar Fadar Shugaban Ƙasa, wannan ita ce ganawar farko ta ƙashin kai tsakanin shugabannin biyu tun bayan rantsar da Wadagni a matsayin shugaban Benin a ranar 24 ga Mayun 2026. Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ne ya tarbi shugaban na Benin bayan isowarsa tare da raka shi zuwa gidan Tinubu.
Shugabannin biyu sun gudanar da wata ganawa ta sirri wadda ta ɗauki kusan mintuna 30, sai dai ba a bayyana cikakkun bayanan abin da suka tattauna ba. Ziyarar ta Wadagni na zuwa ne bayan nasararsa a zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar a Benin ranar 12 ga Afrilu, inda ya gaji tsohon shugaban ƙasar, Patrice Talon.
You must be logged in to post a comment Login