Connect with us

Labarai

Gwamnatin Kano za ta kawo karshen matsalar ruwan sha kafin karshen shekarar 2026

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta tabbatar da kudurinta na kawo karshen matsalar rashin ruwan sha da al’ummar jihar ke fuskanta, ta hanyar kammala manyan ayyukan gyaran hanyoyin samar da ruwa da kuma inganta rumbunan adana ruwa a sassan jihar kafin karshen shekarar 2026.

Mukaddashin Kwamishinan Ruwansha na jihar Kano, kana Kwamishinan Muhalli, Dr. Dahiru Muhammad Hashim, ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a lokacin rangadin duba aikin gyaran rumbun ajiyar ruwa na Gwauran Dutse da ke cikin birnin Kano.

A cewarsa, jihar Kano na da isasshen ruwa da zai wadatar da al’umma baki daya, amma matsalolin lalacewar kayan aikin samar da ruwa da kuma sace-sacen na’urorin rarraba ruwa ne suka haddasa karancin ruwan sha a wasu yankunan jihar.

Kwamishinan ya ce gwamnatin jihar ta dauki matakan gaggawa na gyara manyan rijiyoyi, rumbunan adana ruwa da kuma hanyoyin rarraba ruwa domin tabbatar da cewa al’ummar Kano sun samu wadataccen ruwan sha.

Ya kara da cewa ana ci gaba da aikin gyaran rumbunan adana ruwa masu daukar miliyoyin lita na ruwa, kuma gwamnati na sa ran kammala ayyukan cikin wa’adin da aka tsara, lamarin da zai taimaka wajen magance matsalar karancin ruwa musamman a cikin birnin Kano da kewaye.

Dr. Dahiru Muhammad Hashim ya yi kira ga al’umma da su taimaka wajen kare kayayyakin gwamnati da ake amfani da su wajen samar da ruwa, tare da kai rahoton duk wani yunkurin lalata ko sace kayan aikin domin tabbatar da dorewar ayyukan samar da ruwan sha.

Ya jaddada cewa da zarar an kammala wadannan ayyuka kafin karshen shekarar 2026, matsalar rashin ruwan sha a mafi yawan sassan jihar Kano za ta zama tarihi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!