Ƙetare
Tinubu ya mika ragamar shugabancin ECOWAS ga Julius Maada Bio

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya mika ragamar shugabancin ƙungiyar ECOWAS ga Shugaban kasar Saliyo, Julius Maada Bio.
Tinubu ya mika ragamar shugabancin ne yayin babban taron shugabannin ƙasashen yankin wanda aka gudanar ranar Lahadi a birnin tarayya Abuja.
Shugaba Tinubu ya jagoranci ƙungiyar ta ECOWAS na tsawon shekaru biyu, tun daga watan Yuli na shekara ta 2023, kuma ya kammala wa’adin nasa a taron koli na 67 da aka gudanar a birnin tarayya Abuja.
Shugaba Tinubu, ya ce, ya na da kwarin gwiwa cewa yankin zai ci gaba da tafiya kan turbar zaman lafiya da kwanciyar hankali da kuma ci gaban tattalin arziki.
You must be logged in to post a comment Login