Labaran Wasanni
Tokyo 2020: An baiwa ‘yan kallo dubu 10 damar shiga kowane wasa
Masu shirya gasar guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya da za a gudanar a birnin Tokyo dake kasar Japan mai taken Tokyo 2020, sun ce ‘yan kallo dubu 10 ne aka baiwa damar shiga kallon kowane wasa a kasar.
Hakan na zuwa ne ta cikin wata sanarwa da masu shirya gasar suka fitar don bayyana matsayar kasar ta Japan kan karbar bakuncin gasar yayin da Coronavirus ke kara kamari a wasu kasashen duniya.
Sanarwar ta kuma ce biyo bayan bukatar masana kiwon lafiya, gudanar da wasannin gasar ba tare da da ‘yan kallo ba shine zabi mafi karancin hadari wajen yada cutar COVID-19.
An dai cimma matsayar baiwa ‘yan kallo dubu 10 a kasar damar shiga kallon wasan yayin wani zama da kwararru a fanin lafiya na kasar suka yi da masu shirya gasar don dakile barazanar yaduwar cutar Corona.
Za kuma a fara gasar ne a ranar 23 ga watan Yuli mai kamawa a birnin Tokyo.
You must be logged in to post a comment Login