Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Tokyo 2020: Za mu yi bincike kan musabbabin dakatar da ‘yan wasan Najeriya – Dare

Published

on

Ministan wasanni Sunday Dare ya ce ya bayar da umarnin gudanar da bincike don gano makasudin dakatarwar da aka yiwa ‘yan wasan Najeriya 10 daga gasar Tokyo Olympics.

Sashin kula da nagartar ‘yan wasa na hukumar hana amfani da kwayoyin kara kuzari ne ya dakatar da ‘yan wasan motsa jiki na Najeriya a watan da ya gabata.

An dai dakatar da ‘yan wasan ne sakamakon rashin yin wasu gwaje-gwaje uku da aka tilasta wa kowane dan wasa kafin a fara gasar.

Dare ya ce ma’aikatar zata yi duk mai yiwuwa don tabbatar da ‘yan wasan da aka dakatar sun cimma burinsu na zama ‘yan wasan Olympics.

Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa, ‘yan wasan sun hadar da Ruth Usoro da Favour Ofili da sauran mutane takwas.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!