Labaran Wasanni
Tokyo Olympics: ‘Yan wasan Najeriya sun shiga sansanin daukar horo
‘Yan wasan guje-guje da tsalle-tsalle na Najeriya sun fara shiga sansani daukar horo zagaye na biyu a yankuna uku na fadin kasar nan don shirya wa wasannin gasar Tokyo 2020 Olympic.
A cewar daraktan ‘yan wasan Simeon Ebhojiaye, ‘yan wasan za su kasance sansanin tsawon makonni uku a garin Port Harcourt da Abuja da kuma Yenogoa.
A garin Port Harcourt za a gudanar da wasan tsalle-tsalle da guje-guje na tsawon zagaye 14 karkashin masu horaswa biyu a sansanin yayin da a Abuja za a gudanar da wasannin masu bukata ta musamman inda ‘yan wasan kwallon Tennis 14 da masu daga kayan nauyi 8 suka kasance a sansanin.
Haka kuma akwai ‘yan wasan damben zamani guda 8 da suke a sansanin na garin Yenogoa dake jihar Bayelsa duk a karkashin masu horaswa biyu.
Ka zalika, a zagayen farko an kafa sansanin ne a makarantar horas da malamai dake a garin Pankshin a jihar Plateau inda ‘yan wasa 4 suka sami halartar sansanin.
You must be logged in to post a comment Login