Ƙetare
Trump ya soke zuwan wakilansa Islamabad domin tattaunawa da Iran

Shugaban Amurka, Donald Trump ya tabbatar da soke bulaguron wakilansa zuwa Islamabad domin tattaunawa da wakilan Iran da nufin kawo ƙarshen yaƙin.
Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Trump ya ce: “Na soke tafiyar wakilaina zuwa birnin Islamabad domin tattaunawa da wakilan Iran don kawo ƙarshen yaƙin ƙasar”.
“An ɓata lokaci mai yawa a wannan bulaguro, ana ta kwan gaba kwan baya”.
“Baya ga haka, akwai saɓani da rashin tabbas a tsakanin shugabanninsu, ba wanda ya san wa ke da iko, ciki har da su shugabannin”, in ji shi.
“Kuma mu mun shirya, amma su ba su shirya ba, idan suna buƙatar tattaunawar, sa kira mu”, a cewar Shugaba Trump.
You must be logged in to post a comment Login