Ƙetare
Amurka na shirin janye sojoji 5,000 daga kasar Jamus

Amurka ta sanar da shirin janye kusan sojoji 5,000 daga kasar Jamus cikin watanni 6 zuwa 12 masu zuwa, kamar yadda ma’aikatar tsaron kasar ta Pentagon ta bayyana. Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun sabani tsakanin Amurka da kasashen Turai kan batun yakin Gabas ta Tsakiya.
Shugaban Amurka Donald Trump ya kuma sanar da karin harajin kashi 25% kan motoci da manyan motoci daga Tarayyar Turai, yana mai zargin kasashen Turai da rashin cika yarjejeniyar kasuwanci. Haka kuma ya soki shugaban Jamus Friedrich Merz kan kalamansa game da Iran, inda ya ce bai fahimci lamarin ba.
Trump ya dade yana matsa lamba ga kasashen Turai su dauki nauyin tsaron kansu maimakon dogaro da Amurka, yana mai barazanar rage yawan sojojin Amurka a nahiyar. Ya kuma nuna yiwuwar janye sojoji daga kasashen Italiya da Spain saboda rashin goyon bayan da suke bayarwa.
Sai dai gwamnatin Jamus ta ce ta shirya fuskantar wannan sauyi, tana mai jaddada muhimmancin sansanonin sojin Amurka da ke kasar, musamman Ramstein Air Base. Kasashen Turai sun kuma jaddada cewa kasancewar sojojin Amurka na da matukar muhimmanci ga tsaron yankin, musamman bayan mamayar Ukraine da Rasha ta yi.
You must be logged in to post a comment Login