Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Tsaftar muhalli: Za mu ɗauki matakin hukunci a kan hukumar RUWASA – Dr. Getso

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ce za ta ɗauki matakin hukunci ga hukumar samar da ruwan sha a karkara da tsaftar muhalli ta RUWASA.

Matakin ya biyo bayan nuna halin ko’in kula da tsaftar muhallin su da suka yi.

Kwamishinan muhalli Dakta Kabiru Ibrahim Getso ne ya bayyana hakan a yau, lokacin da ya jagoranci tawagar tsaftar muhalli zuwa hukumar.

Za mu yi hadin guiwa da wani kamfanin aikin tsaftar muhalli a Kano – Ganduje

Dakta Kabiru Getso ya ce, yanayain da aka samu hukumar na rashin tsaftar muhalli abin takaici ne, kasancewar ta guda daga cikin masu ruwa da tsaki wajen tsaftar muhalli.

“Na daɗe banga abin takaici irin na yau ba a ɓangaren tsaftar muhalli, abinda hukumar RUWASA ta yi abin Allah wadai ne, kuma ba za mu lamunta ba” in ji Getso.

Ya ce, ma’aikatar muhalli ta basu wa’adin kwanaki uku da su tabbatar sun tsaftace muhallin su, ko kuma su fuskanci hukunci.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!