Labarai
Tsaftar muhalli: Za mu sake nazaratar duban kasuwanni a Kano
Gwamnatin jihar Kano za ta sake nazartar kwamitin da ke kula da tsaftar kasuwannin jihar a wani mataki na inganta tsaftar muhalli a kasuwannin.
Kwamishinan muhalli Dakta Ibrahim Getso ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a lokacin da ya ziyarci kasuwar Tarauni ɓangaren mayanka.
Getso ya ce, ba zai yiwu a ce sau ɗaya a wata za’a riƙa bibiyar kasuwanni don ganin yadda suke tsafta ba.
“Mun je mun duba wannan kasuwa, mu zagaywa musamman ma guraren da ake yanka dabbobi, gaskiya ba mu ga yadda muke so ba, domin kuwa wajen da ake yanka manyan dabbobi wari yake kuma duk ya farfashe”.
Ganduje zai ƙulla alaƙa da ƙasar Denmark domin sarrafa shara zuwa dukiya
“Wannan ya nuna cewa akwai buƙatar mu sake zama da shugabannin kwamitin tsaftar muhalli a kasuwanni, don duba yiwuwar ƙara wasu kwanakin da za a riƙa ziyaratar kasuwanni ba sai ƙarshen wata ba”.
A Juma’ar ƙarshen kowanne wata ne ake gudanar da duban tsaftar muhalli na kasuwanni, ma’aikatun gwamnati, tashoshin mota makarantu da sauran su.
You must be logged in to post a comment Login