Labarai
Tsaro: Al’ummar Sharfaɗi da kewaye sun kafa zauren yaƙi da aikata laifuka
Mai girma wakilin Gabas Alhaji Faruk Sani Yola ya nemi iyaye da su bai wa jami’an tsaro haɗin kai domin yaƙi da aikata laifuka a unguwannin birnin Kano.
Wakilin Gabas ya bayyana hakan ne, a yayin wani babban taron zauren haɗin kan unguwannin Sharfaɗi da kewaye da aka yi a ranar Alhamis.
A cewar sa, lokaci ya yi da iyaye za su daina zuwa neman beli idan an kama ƴaƴan su da laifin ta’ammali da miyagun ƙwayoyi.
Alhaji Ibrahim Auwalu Uba shi ne mai unguwar Sharfaɗi da ya jagoranci shirya taron ya ce, an cimma matsaya tsakanin jami’an tsaro da al’ummar unguwanni domin yin aiki tare wajen yaƙi da masu aikata laifuka.
A nasa ɓangaren ɗaya daga cikin manyan unguwannin Alhaji Aliko Shu’aibu Mukhtar ya ce, za a zauna a samar da tsarin da zai samar wa matasan aikin yi.
Masu Unguwannin da suka halarci taron sun haɗa da, Sharfaɗi da Kurna Maɗatai, da Cheɗiyar Ƙuda da Agadasawa sai kuma unguwar Soronɗinki da Satatima da kuma Kurawa.
Taron ya samu halartar masu ruwa da tsaki na al’ummar unguwannin da jami’an tsaro.
You must be logged in to post a comment Login