Labarai
Tsaro: Buhari ya gana da Abdussalam Abubakar
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da tsohon shugaban mulkin soji na kasar nan janar Abdussalami Abubakar mai ritaya yau a fadar Asorok.
Mai taimakawa shugaban kasa kan harkokin yada labarai na zamani Bashir Ahmed ne ya bayyana haka ta cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na twita.
Sai dai mai taimakawa shugaban kasar bai yi karin bayani kan dalilan da ya sanya tsohon shugaban mulkin sojin ya ziyarci shugaba Buhari ba.
A baya-bayan nan dai an jiyo tsohon shugaban kasar yana bayyana damuwar sa kan tabarbarewar tsaro a kasar nan.
You must be logged in to post a comment Login