Connect with us

Labarai

Tsaro: Za mu ɗauki sabbin Kuratan ƴan sanda dubu 20 a ƙasar nan – IG Usman Alƙali

Published

on

Sufeton ƴan sandan ƙasar nan Usman Alkali Baba ya ce nan ba da jimawa ba za a dauki ƙarin kuratan ƴan sanda dubu ashirin a faɗin ƙasar nan.

Usman Alƙali ya bayyana hakan lokacin da ya kai ziyara ga gwamnan jihar Oyo Seyi Makinde a ranar Talata.

Sufeton ya kuma ce, rundunar yan sandan Najeriya na buƙatar ƙari da kuma samar da kayayyakin aiki don yaki da matsalar tsaro.

Kazalika ya tabbatar da cewa tuni shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya amince da ɗaukan ƙarin sabbin jami’an ƴan sandan,duk da an samu jinkiri wajen fara ɗaukan su.

Har ma ya jaddada cewa kowacce ƙaramar hukuma a faɗin ƙasar nan za a ɗauki kuratan ƴan sanda kuma a ƙaramar hukumar ta su za su yi aiki.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!