Connect with us

Labarai

Jami’ar Kaduna ta musanta yin murabus din Malamanta fiye da 200

Published

on

Shugaban Jami’ar Jihar Kaduna Farfesa Abdullahi Ibrahim Musa, ya musanta ikirarin reshen Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta kasa ASUU na cewa fiye da malamai 200 sun bar jami’ar saboda rashin samun kyakkyawar kula daga gwamnatin jihar.

 

shugaban , ya bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da ya fitar a aya-bayan nan kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.

 

Ta cikin sanarwar, Jami’ar ta bayyana ikirarin a matsayin mai ruɗarwa kuma wanda bai yi dai-dai da halin da ake ciki a jami’ar ba.

 

Hakan dai, ya biyo bayan wani taron manema labarai da kungiyar ASUU reshen jami’ar ya gudanar, inda ƙungiyar ta bai wa Gwamnatin Jihar Kaduna wa’adin makonni biyu domin aiwatar da yarjejeniyar da suka kulla da gwamnatin tarayya ta shekarar 2025, tare da magance wasu matsalolin walwalar ma’aikata.

 

Farfesa Abdullahi Ibrahim Musa, ya ce, sauya wurin aiki da malaman jami’a da sauran ma’aikata ke yi tsakanin jami’o’i abu ne da ya zama ruwan dare a duniya, don haka bai kamata a ɗauke shi a matsayin hujjar rashin kyawun yanayin aiki a jami’ar ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!