Manyan Labarai
Tsoho mai shekaru 70 da ke safarar kwayoyi ga ‘yan ta’adda ya fada komar NDLEA
Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta cafke wani tsoho mai shekaru 70 a Jihar Niger da ke safarar kwayoyi ga ‘yan Boko Haram da kuma ‘yan bindiga.
Wannan na cikin wata sanarwa da daraktan yada labaran hukumar Femi Baba Femi ya fitar yau a Abuja.
Sanarwar ta ce mutumin mai suna Muhammad Rabi’u, ya fito ne daga garin Dallawa na Jihar Agadez a Jamhuriyar Nijar, kuma sun kama shi ne dauke da tarin kwayoyin a Jebba.
Ta cikin sanarwar, Muhammad Rabi’u ya ce yana sana’ar safarar fatu da kiraga ne daga Jamhuriyar Nijar yana sayarwa a Jihar Lagos, sannan ya sayi kwayoyin ya kaiwa ‘yan ta’adda.
You must be logged in to post a comment Login