Siyasa
Tsohon kwamishinan ayyuka na Kano Aliyu Wudil ya fice daga APC zuwa NNPP
Tsohon kwamishinan Ayyuka na jihar Kano Injiniya Aminu Aliyu Wudil ya fice daga jami’iyyar APC zuwa NNPP.
Aliyu Wudi wanda a baya kwamishinan ayyuka ne a gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ya sanar da hakan ne a wani rubutu da hadimin Sanata Kwankwaso Saifullahi Hassan ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Aminu Aliyu Wudil ya ziyarci Sanata Kwankwaso a ranar Talata a gidansa Abuja.
You must be logged in to post a comment Login