Connect with us

Kiwon Lafiya

Tsohon shugaban kasa Shagari ya rasu

Published

on

Tsohon shugaban kasar nan a jamhuriya ta biyu Alhaji Shehu Shagari ya rasu da yammacin nan a babban asibitin kasa da ke birnin tarayya Abuja.

Daya daga cikin jikokin tsohon shugaban kasar mai suna Bello Shagari ya wallafa a shafinsa na twitter cewa, Alhaji Shehu Shagari ya rasu ne biyo bayan ya yi fama da wata gajeriyar jinya.

Marigayin dai shi ne shugaban kasa a jamhuriya ta biyu daga shekarar 1979 zuwa 1983, inda soji suka yi masa juyin mulki.

Haka kuma wakilin freedom rediyo da ke Sokoto Abba Lawal Kurmawa ya tabbatar da labarin.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!