Kasuwanci
TUC ta bai wa gwamnati kwanaki 14 kan ta janye yunkurinta na karin kudin Mai

Ƙungiyar ƙwadago ta TUC ta yi watsi da matakin gwamnatin tarayya na ƙara kaso 5 cikin 100 kan farashin kowacce litar mai, ta na mai kwatanta hakan a matsayin ganganci ga tattalin arzikin ƙasa.
A cewar gwamnatin tarayyar ta ɗauki wannan mataki ne don samun kuɗaɗen shiga da za’a yi amfani da su wajen gina hanyoyi da sauran manyan ayyuka a ƙasar nan.
Tuni dai ƙungiyar ta bai wa gwamnatin wa’adin kwanaki 14 da ta janye wannan matakin, ko kuma ta ɗauki matakin da take ganin ya dace.
A cewarta cikin matakin da zata ɗauka har da rufe manyan sassan gwamnati musamman masu samar da kuɗaɗen shiga.
Ta cikin wata sanarwa da Festus Osifo da kuma Nuhu Toro shugabannin ƙungiyar suka sanyawa hannu, sun ce a halin da ake ciki ƴan Najeriya na cikin ƙangin biyan haraje-haraje barkatai.
Shugabannin ƙungiyar ƙwadagon, sun ce sabon harajin ba abu ne da zai yiwu ba, don haka ya zama wajibi gwamnati ta dakatar da shi.
You must be logged in to post a comment Login