Labarai
Tuna baya: a ranar talata sanatoci sun amince Buhari ya ciyo bashin dala biliyan daya da rabi
Majalisar dattijai a shekaran jiya talata ta amincewa shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya ciyo bashin dala biliyan daya da miliyan dari biyar daga kasashen waje.
Hakan ya biyo bayan amincewa da sakamakon rahoton shugaban kwamitin kula da basukan cikin gida da na ketare na majalisar dattawa, Clifford Odia ya gabatar ya yin zaman majalisar.
A watan Mayun shekarar da ta gabata ta 2020 ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika da bukatar ciyo bashin daga kasashen waje ga majalisar dattijai, don bai wa gwamnati damar samun kudade da za ta cike gibin kasafin kudin shekarar.
Ta cikin wasikar neman bashin gwamnatin tarayya ta ce za ta yi amfani da kudaden ne wajen gudanar da wasu muhimman ayyukan raya kasa da taimakawa wasu jihohi da ke halin tagayyara sakamakon cutar corona.
You must be logged in to post a comment Login