Kiwon Lafiya
UN:Ta nuna damuwarta game da farfadowar Boko haram
Majalisar dinkin duniya ta nuna damuwarta game da sake farfadowar mayakan Boko-Haram a yankin arewa maso gabashin kasar nan.
A cewar majalisar tun bayan da kungiyar Boko haram ta dawo da kaiwan hare-hare ta janye ma’aikatan ta na jinkai dari biyu da sittin, wanda ta ce hakan ya yi tasiri matuka wajen kara ta’azzara lamuran jinkai.
Majalisar ta kuma nuna damuwara game da Karin kwararar ‘yan gudun hijira wadanda ta ce ya zuwa yanzu wadanda suka isa garin Maiduguri daga Baga sun kai dubu talatin.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da yawun majalisar dinkin duniya a Najeriya, Samantha Newport.
Sanarwar ta kuma ruwaito babban jami’in majalisar dinkin duniya a kasar nan Mr Edward kallon na cewa, akwai bukatan gwamnatoci da ke yankin tabkin Chadi su rika aiki tare don kawo karshen matsalar ba.