Connect with us

Ƙetare

Vladimir Putin ya gana da wakilan Amurka kan yakin Ukraine

Published

on

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya gana da wakilan Amurka Steve Witkoff da Jared Kushner a fadar Kremlin, inda tattaunawar ta dauki kusan sa’o’i uku.

Putin ya ce halin da ake ciki a yakin Ukraine yana da wahala, amma ya yaba da kokarin Shugaban Amurka Donald Trump na ganin an kawo karshen yakin.

Kremlin ta ce Putin ya umarci sojojin Rasha da kada su kai hari Kyiv na tsawon kwanaki uku, yayin da wakilan Amurka za su tafi Ukraine domin ci gaba da tattaunawa. Shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskiy ya kuma ce kasarsa a shirye take ta dakatar da kai hare-hare kan Moscow har zuwa ranar Litinin.

Sai dai har yanzu akwai babban sabani tsakanin Rasha da Ukraine kan yadda za a kawo karshen yakin. Rasha na neman Ukraine ta mika wasu yankuna da Moscow ke ikirarin mallakarsu, yayin da Ukraine ta ki amincewa da hakan.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!