Connect with us

Ƙetare

Mutane 23 sun mutu yayin da 113 suka kamu da cutar kwalara a Sudan

Published

on

Ana fargabar mutuwar mutane ashirin da uku, yayin da fiye da dari uku da goma suka kamu da cutar kwalara ko kuma ake zargin sun kamu da ita, a wasu yankuna biyu na Kordofan ta yamma a Sudan.

Kungiyar agaji ta Dar Hamar Emergency Room ce ta bayyana hakan, tana mai cewa cutar ta fi kamari a yankunan Humeir da Hilla Hussein.

Kungiyar ta ce a Humeir, ana kula da mutane 120 da ake zargin sun kamu da kwalara, inda mutane 11 suka mutu.

A Hilla Hussein kuwa, an samu sama da mutane 190 da suka kamu da cutar, yayin da 12 suka mutu.

Kungiyar ta kuma yi gargadin cewa cibiyoyin kiwon lafiya na fama da Karancin magunguna da ruwan jinya, lamarin da ke kara ta’azzara matsalar.

Haka kuma, ta ce karancin abinci ya yi tsanani, har wasu iyalai ke amfani da abincin dabbobi wajen ciyar da ’ya’yansu.

Kungiyar ta yi kira ga hukumomin lafiya da kungiyoyin agaji da su gaggauta kai magunguna da kayan abinci ga mutanen yankin.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!