Connect with us

Ƙetare

Wani Ba’amurike ya samu ’yanci bayan garkuwa da shi a Nijar

Published

on

Wani Ba’amuriken Kirista mai wa’azi, Kevin Rideout, ya samu ’yanci bayan shafe sama da watanni tara a hannun masu garkuwa da mutane a Jamhuriyar Nijar.

Kungiyar SIM International da yake yi wa aiki ce ta tabbatar da sakin nasa, inda ta ce a yanzu yana cikin koshin lafiya kuma jami’an Amurka ne ke kula da shi.

Rahotanni sun ce an yi garkuwa da Rideout ne a watan Oktoban 2025, a wajen gidansa da ke birnin Yamai, babban birnin Nijar, inda wasu mutane uku dauke da makamai suka sace shi zuwa yankin Tillaberi da ke yammacin kasar.

Har yanzu ba a bayyana yadda aka samu sakin nasa ba, ko kuma wadanda suka yi garkuwa da shi.

A baya dai an yi zargin cewa mayakan kungiyoyin masu ikirarin jihadi, ciki har da kungiyar Jama’at Nusrat al-Islam wal-Muslimin, mai alaka da Al-Qaeda, na iya kasancewa a bayan sace shi.

Rideout, wanda kuma matukin jirgi ne, ya kwashe shekaru 19 yana aikin wa’azi a Nijar, tare da yi wa SIM International aikin tukin jirgi.

Kungiyar ta ce sakin nasa babban labari ne mai dadi, bayan watanni da dama na rashin tabbas kan halin da yake ciki.

Ta kuma ce nan ba da jimawa ba zai sake haduwa da matarsa, ’ya’yansa da sauran ’yan uwansa, tare da rokon jama’a da su bai wa iyalinsa damar samun nutsuwa bayan tsawon lokacin da suka yi a rabe.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!