Labaran Wasanni
WA U-20 Championships: Najeriya ta lashe kyautar Zinare

Tawagar ‘yan wasan guje-guje da tsalle-tsalle na Najeriya ta yi nasarar lashe kautar zinare a gasar guje-guje da tsalle-tsalle ta ‘yan kasa da shekaru 20 ta duniya.
Yanzu haka dai ana cigaba da gudanar gasar a birnin Nairobi dake kasar Kenya.
Wannan ce nasara ta farko da Najeriya ta samu tun bayan shekarar 2008 da ‘yar wasa Folashade Abugan ta taba lashe kyautar a kasar Poland.
You must be logged in to post a comment Login