Labarai
Wada Sagagi ya yi watsi da ƙaddamar da Kwamitin Kamfen ɗin PDP a Kano
Shugaban jam’iyyar PDP na Kano Alhaji Shehu Wada Sagagi ya yi watsi da kwamitin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar da aka ƙaddamar a Kano.
Hakan na cikin wata sanarwa da mashawarcin jam’iyyar kan harkokin shari’a Barista Isah Wangida ya fitar a ranar Lahadi.
Sanarwar ta nuna cewar, taron ƙaddamar da Dr. Adamu Yunusa Ɗangwani a matsayin shugaban kwamitin yakin neman zaben jam’iyyar a Kano haramtacce ne.
Barrista Wangida ya kuma yi watsi da waɗanda suka bayyana kansu a matsayin kwamitin riƙon jam’iyyar, yana mai cewa hakan ya ci karo da hukuncin Kotu.
Labarai masu alaƙa:
Wada Sagagi ya nemi Shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa yayi murabus
Kano: Kotu ta karɓe takarar Sadiq Wali ta bai wa Muhammad Abacha
Ya ce, Shehu Wada Sagagi shi ne halattaccen shugaban PDP a Kano bisa hukuncin da Kotu ta yi.
Ko a baya-bayan nan Babbar Kotun tarayya ta tabbatar da ɗan takararmu Alhaji Mohammed Sani Abacha wanda haka ke nufin mu kaɗai ne shugabanni a cewarsa.
A ƙarshe ya ce tuni suka garzaya Kotu da ƙorafi kan wannan taro da aka yi ba bisa ƙa’ida ba.
Ya kuma kira ga ƴan jam’iyyar da su kwantar da hankalinsu su ci gaba da biyayya ga umarnin shugabanni.
You must be logged in to post a comment Login