Coronavirus
Wadanda Corona ta hallaka a Kano sun zarce na Abuja
Gwamnatin jihar Kano ta tabbatar da mutuwar mutane 18 sanadiyyar cutar Covid-19, wannan adadi dai ya zarce na wadanda cutar ta hallaka a birnin tarayya Abuja.
A kididdigar da cibiyar dakile cutuka masu yaduwa ta kasa NCDC ta fitar a daren ranar Jumu’a ta ce mutane 4 ne suka rasa ransu sanadiyyar cutar Covid-19 a birnin tarayya Abuja.
Birnin Abuja dai shi ne gari na biyu da cutar ta fara bulla a Najeriya, sai dai sannu a hankali yanzu jihar Kano ta karbe kambun yawan masu dauke da cutar, domin kuwa yanzu Kano ita ce ke mataki na 2 a jihohin dake da yawan masu Corona a Najeriya.
Karin labarai:
Labari mara dadi: Wadanda suka kamu da Corona sun haura 500 a Kano
Ma’aikatan jinya 18 sun kamu da Corona a Kano
Alkaluman NCDC na ranar Jumu’a ya ce mutane 336 ne suka kamu da cutar Covid-19 a birnin na Abuja inda mutum 40 daga ciki aka sallamesu bayan da suka warke, mutane 4 kuma suka rasa ransu, saura mutane 292 wadanda suke karbar kulawa daga jami’an lafiya.
A jihar Kano kuwa yanzu ana da mutane 547 da suka kamu da cutar, mutum 20 daga ciki sun warke, 18 kuma sun rasu, sauran mutane 509 na cigaba da karbar kulawa a cibiyoyin killace masu dauke a cutar Covid-19 dake Kano.
You must be logged in to post a comment Login