Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

NCDC : Yawan masu dauke da cutar Corona ya zarta dubu 69 a Najeriya

Published

on

Hukumar dakile yaduwar cutuka ta kasa NCDC ta ce, a jiya Lahadi an samu Karin mutane 318 masu dauke da cutar a Corona a jihohi 13 na kasar nan da birnin tarayya Abuja.

Haka na cikin sanarwar da NCDC ta fitar a shafinta na Twitter, inda ta ce, yanzu haka adadin wadanda suka kamu da cutar ya kai 69,255.

Mutum 64,774 sun warke, sai guda 1,180 da cutar ta hallaka.
A nan Kano ma ma’akatar lafiya ta jiha ta ce, an samu Karin mutum 14 masu cutar cikin 348 da aka yiwa gwaji a jiya Lahadin.

Zuwa yanzu mutane 1,819 suka kamu da cutar a Kano, an sallami 1,713 bayan da suka warke, sai mutum 54 da cutar ta yi ajalin su.

Yanzu haka masu Corona 52 suka rage wadanda ke jiyya a nan Kano, a cewar ma’aikatar lafiyan.
To nan gaba kadan, zaku ji yadda wasu hukumomi suka musanta wani rahoton gwamnatin Kano kan yawaitar masu cutar ta Corona.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!