Connect with us

Coronavirus

Wadanda suka kamu da Corona a Najeriya sun kai 4,787

Published

on

Hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta kasa NCDC ta ce a ranar Talatarnan an samu gano karin mutane 146 dake dauke da cutar Covid-19 a sassa daban-daban na kasar.

Wannan kari da aka samu ya kai jimillar wadanda suka kamu da cutar a kasarnan zuwa 4,787.

Kididdigar da NCDC ta fitar a daren Talata tace mutane 158 ne suka ransu sanadiyyar cutar a fadin kasarnan.

Haka kuma mutane 959 ne suka warke sarai daga cutar bayan samun kulawa daga jami’an lafiya.

Labarai masu alaka:

An yiwa mutane 346 gwajin Corona a Sokoto

Ganduje ya kaddamar da rabon “Face Mask” miliyan biyu ga Kanawa

Idan zaku iya tunawa dai a ranar Talata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince kan kwamitin yakar cutar Corona na kasar da ya karbi maganin gargajiya na cutar da kasar Madagascar ta samar da Tazargade domin ganin yiwuwar amfani dashi a kasar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!