Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Coronavirus

Labari mai dadi: Masu Corona 74 sun warke a Kano

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta tabbatar da cewa mutane 74 sun warke daga cutar Covid-19 a jihar.

Ma’aikatar lafiya ta Kano ta sanar a daren ranar Talata da karfe 11:50 na dare cewa a ranar kadai an samu karin mutane 27 da aka gano suna dauke da cutar a Kano.

Yazuwa yanzu mutane 693 ne suka kamu da cutar a jihar Kano.

83 daga cikin sun warke sai 33 da suka rigamu gidan gaskiya.

Saura mutane 586 wadanda suke cigaba da karbar kulawar jami’an lafiya a cibiyoyin killace masu dauke da cutar dake Kano.

labarai masu alaka:

Covid-19: Wadanda suka warke daga Corona a Kano sun zarce na Abuja

Yadda cibiyar gwajin Corona ta Dangote ke aiki a Kano

A ranar Litinin da ta gabata ne gwamnatin Kano ta sanar da tsawaita dokar kulle da zama gida a jihar har tsawon mako guda.

A wani bangaren kuma a ranar Talata ne gwamnan jihar Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya gana da sarakunan gargajiya na Kano, inda ya nemi su mayar da hankali wajen wayar da kan al’umma kan cutar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!