Coronavirus
Wadanda suka kamu da Corona sun kusa 4,000 a Najeriya
Hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta kasa NCDC ta ce cikin yini guda an samu karin mutane 386 da suka kamu da cutar Covid-19 a sassa daban-daban na kasarnan.
Wannan adadi shine mafi yawa da aka samu cikin yini guda tun bullar cutar a kasar zuwa yanzu.
Kididdigar da NCDC ta fitar a daren jumu’ar nan tace a ranar an samu karin mutane 176 da suka kamu da cutar a jihar Legas, sai jihar Kano da aka samu karin mutane 65, Katsina mutum 31, birnin tarayya Abuja karin mutane 20 sai jihar Borno da mutum 17, jihar Bauchi ke biye mata baya da mutane 15 sai jihar Nassarawa mai mutane 14.
Jihar Ogun na da mutane 13, Plateau 10, Oyo 4, Sokoto ma mutum 4, sai Rivers da ita ma ta samu karin mutane 4, jihar Kaduna ta samu mutum 3.
Jihar Edo, Ebonyi da Ondo, kowacce ta samu karin mutane bi-biyu.
Yayinda jihohin Enugu, Imo da Gombe da kuma Osun suka samu karin mutane guda-guda kowannen su.
Yanzu haka dai NCDC ta ce mutane 679 ne aka sallama bayan sun warke da cutar a sassa daban-daban na kasarnan.
Yazuwa yanu mutane 117 ne suka rasa ransu sanadiyyar cutar ta Covid-19 a Najeriya.
Karin labarai:
Wadanda Corona ta hallaka a Kano sun zarce na Abuja
Labari mara dadi: Wadanda suka kamu da Corona sun haura 500 a Kano
You must be logged in to post a comment Login