Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Coronavirus

Covid-19: Masu Corona sun kai 3,145 a Najeriya

Published

on

Hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta kasa NCDC ta ce yanzu haka mutane 3,145 ne suka kamu da cutar Covid-19 a kasarnan.

A jadawalin lissafin wadanda suka kamu da cutar da NCDC ta fitar a baya-bayan nan ta ce a ranar Laraba kadai an samu karin mutane 195 da suka kamu da cutar a sassa daban-daban na kasarnan.

A Kididdigar ta ranar Laraba jihar Legas ke kan gaba da mutane 82, sai jihar Kano da ta samu karin mutane 39, Jihar Zamfara ta samu karin mutane 19, sai Sokoto mai mutane 18.

Karin labarai:

Adadin masu Corona sun haura 100 a jihar Borno

Ma’aikatan lafiya 14 sun kamu da Corona a Katsina

Jihar Borno ta samu karin mutum 10, birnin tarayya Abuja ya samu karin mutane 9, jihar Oyo mutum 8, sai Kebbi da ta samu karin mutane 5, haka abin yake a jihar Gombe ita ma karin mutum 5.

Jihar Ogun ta samy karin mutum 4, sai jihar Katsina da ta samu karin mutum 3, Kaduna ta samu mutum 1 sai jihar Adamawa itama ta samu karin mutum 1.

Yanzu haka dai NCDC ta ce akalla mutane 534 ne suka warke daga cutar Coronavirus a sassan kasarnan.

Sannan mutane 103 ne suka rasa ransu sanadiyyar cutar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!