ilimi
WAEC ta sanya ranar fara rubuta jarrabawa a bana
Hukumar shirya jarrabawar kammala sakandire ta yammacin Afrika WAEC ta sanya ranar 16 ga watan Agusta zuwa 30 ga watan Satumba a matsayin ranakun da ɗaliban bana za su rubuta jarrabawar.
Mai magana da yawun hukumar Patrick Areghan ne ya bayyana hakan, yana mai cewa, tsaikon da aka samu na rubuta jarrabawar ya faru ne sakamakon bullar annobar corona da ta rusa jadawalin karatu na shekarar 2021 da 2022.
Patrick ya ce, akwai rashin fara yiwa ɗaliban rijista kamar yadda aka tsara, kuma ake rubuta jarrabawar a matannin Maris da Afrilu zuwa Mayu.
Hukumar ta WAEC ta ce a bana ɗalibai sama da miliyan daya da dubu dari biyar da saba’in da uku, da dari bakwai da tamanin da tara ne zasu rubuta jarrabawar a makarantu dubu goma sha tara da dari hudu da ashirin da biyar da ake da su a fadin ƙasar nan.
You must be logged in to post a comment Login