Labaran Kano
Waiwaye: Shekaru 14 cif da kisan Hajiya Sa’adatu Rimi
An dai kashe Hajiya Sa’adatu Rimi ne a ranar 14 ga watan Janairun shekara ta 2006 a gidanta dake nan Kano cikin dare.
Al’ummar jihar Kano sun shiga rudani sosai da jin mutuwarta, kasancewar ana tsaka da guguwar siyasa a lokacin.
Idan mai karatu bai mance ba da jin rasuwarta ta ne rundunar ‘Yan sanda ta fara binciken mummunan kisan da aka yi wa Hajiya Sa’adatu Rimi.
An tsinci gawar Hajiya Sa’adatu Abubakar Rimi ranar Asabar a cikin falon dakinta, kuma a bisa dukkan alamu an yanka ta ne, kamar yankan Rago.
A lokacin kisan, kowa na kallon an yi hakan ne saboda karuwar tankiyar siyasa a arewacin kasar nan, kasancewar wannan mumunanr dabi’ar tafi kamari ne a yankin kudancin Najeriya.
‘Yar uwar Hajiya Sa’adatu Rimi da ake kira da Halima dake gidan a lokacin da al’amarin ya faru ta shaidawa manema labarai cewa kafin kisan nata sun ji karar wani abu da karfi a jikin kofa, kuma da suka fito su binciki abinda ya faru sai suka ga Hajiya Sa’adatu kwance jina-jina.
‘’Ta ce mutanen sun zo ne suka kashe ta kawai, amma ba su dauki komai a gidan ba’’
Rahotanni sun bayyana cewar, a washe gari maraicen Asabar ne aka yi jana’izar marigayiyar a kofar gidan mai martaba Sarkin Kano, marigayi Alhaji Ado Bayero.
Wadanda suka halarci jana’izar sun hada da tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar, da tsofaffin gwamnonin Jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau da Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso.
Tun da fari, jikin mutane yayi la’asar a wurin taron cikar shekaru Arba’in da mutuwar Sardaunan Sakkwato, Ahmadu Bello, a lokacin da labari ya karade sassan kasar nan da kuma zauren taron kan kisan matar Abubakar Rimi.
Da jin mutuwar ta ta ne sai marigayi Alhaji Abubakar Rimi tare da tsohon gwamna jihar Kano Ibrahim Shekarau suka bar taron don halatar jana’izar marigayiyar.
Ana dai zargin cewa, wasu bata gari ne suka shiga gidan marigyiyar cikin dare suka yi mata yankar rago yayin da jami’an tsaro da wasu hadiman gidan ta suka tarar da ita cikin jini shame-shame a kwance.
Gwamnatin Kano dai ta sauya sunan Kwalejin ilimi ta jiha zuwa sunan marigayiyar Sa’adatu Rimi don tunawa da irin gudunmawar da ta bayar.
Daga nan Freedom Rediyo muna Addu’ar Allah ya jikan marigayiyyar Hajiya Sa’adatu Rimi ya sa Aljanna ce makomar ta.
Labarai masu alaka: