Labarai
Wajibi ne mu bi kadun cin zarafin jami’anmu- KAROTA
Hukumar Kula da Zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kano KAROTA, ta cafke guda daga cikin waɗanda ake zargi da far wa jami’anta.
Hukumar ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da jami’inta na yaɗa labarai Nabilusi Abubakar Kofar Na’isa ya fitar a yau Litinin.
Sanarwar ta ce, Hukumar ta sami nasarar kama matashin mai suna Saifullahi Haruna jim kadan bayan da wasu ɓata gari sun far wa jami’an hukumar da suke bincike ababen hawa a kan titin Panshekara cikin burnin Kano
Haka kuma sanarwar ta ƙara da cewa Wasu ɓata garin matasa ne suka far wa jami’an nata da misalin karfe 3 na dare a kan titin Panshekara.
Sanarwar ta KAROTA, ta kuma ce, Hukumar ba za ta zuba ido ta kyale ana cin zarafin jami’anta ba, domin kuwa aiki suke bisa tsarin doka
Haka kuma sanarwa ta ruwaito cewa, Hukumar ta miķa wadanda ta kama wajen Baturen Yansandan yankin da abin ya faru domin fadada bincike tare da daukar matakin kama ragowar domin gurfanar da su a gaban shari’a.
Ta cikin sanarwar kuma, ta ruwaito cewa shugaban hukumar ta KAROTA Injiniya Faisal Mahmud Kabir ya ce, ya zama wajibi hukumar ta gode wa al’ummar Kano musamman wadanda suke ankarar da ita wani gyara idan buķatar hakan ta taso
Ya ce ķofar Hukumar a bude ta ke ga duk wanda ya ga wani gyara ko shawara ya sanar da ita a shalkwatarta ko kuma ta lambar waya 08023608861.
You must be logged in to post a comment Login