Labaran Kano
Wani Baturen ‘’Yansanda ya taba karya malamin makaranta saboda ya mallaki sabuwar mota
Tun kafa kungiyar kwato hakkin dan Adam ta network for justice a shekaru 26 da suka wuce ta yi sanadin ceto mutane da dama daga kangin zalunci.
Tsohon shugaban kungiyar kuma mamba a yanzu Farfesa Sadiq Isa Rada ne ya bayyana haka a tattaunawa da yayi da shirin Barka da Hantsi na nan gidan rediyan Freedom.
Sadiq Isa Rada yace akwai wani lokaci da wani jami’in dansanda ya karairaya wani malamin makaranta sakamakon ya sayi sabuwar mota.
Farfesa Rada yace dalilin da yasa baturen ‘’yansandan dake aiki a garin Daura ta jahar Katsina ya karya malamin shi ne yana ganin bashi da damar da zai iya sayan sabuwar mota.
Yace sun taba nemawa wani direba hakkin sa lokacin da wani soja ke cikin maye ya taka wani direba.
Farfesa Rada ya kara da cewa kungiyar ta network for justice Farfesa Attahiru Jega ne da Farfesa Auwalu Hamisu Yadudu da Farfesa Na’iya Sada da Bala Abdullahi suka kafa ta.