Labarai
Ko kun san rukunin ma’aikatan da Buhari zai dauka aiki na din-din-din ?
Gwamnatin tarayya ta bayar da umarnin daukar ma’aikata sama da dubu 30 aikin din-din-din.
Wadanda za’a dauka aikin su ne wadanda suka karanci bangaren aikin Gona da kuma Kimiyya.
Sakataren zartaswa na hukumar bunkasa aikin noma Ta kasa, Prince Paul Ikonne, ya sanar da haka a Abuja.
Prince Paul Ikonne, ya ce ma’aikatan da za a dauka aikin, za su rinka auna kasa da kuma bayar da shawarwari ga manoma.
Sai dai ya ce ko wanne manomi zai biya naira 500 a matsayin kudin Awun kasar da akaiwa gonarsa, kana kuma bayan horas da ma’aikatan, za a basu kayan aikin da za suyi amfani da su wajen aikewa hukumar bayanai kai tsaye ofishinta dake Abuja.
You must be logged in to post a comment Login