Connect with us

Labarai

‘Yan tadda sun kashe baturen ‘yan sanda a Sokoto

Published

on

Wasu da ake zargin ‘yan tada kayar baya ne sun kashe wani baturen ‘yan sanda dake garin Madi cikin karamar hukumar Tangaza ta jihar Sokoto.

Har ila yau ‘yan bindigar sun kuma kashe wani jami’in dan sanda, inda daga bisani suka yi garkuwa da wasu matan wani hamshakin dan kasuwa a yankin.

‘Yan bindigar sun shiga yankin da misalin karfe 1 na daren jiya Laraba, inda suka yiwa ‘yan sandan kwanton bauna dai-dai lokacin da suke kokarin kubutar da wanda aka yi garkuwa da su.

Rahotanni na nuni da cewa ‘yan tada kayar bayan sun kuma tsere da bindigogin jami’an ‘yan sandan bayan kashe su.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!