Kiwon Lafiya
Wasu gwamnonin Arewa zasu tallafa wa Najeriya wajen hako mai a jihohin su
Gwamnonin jihar Sokoto da Kebbi Da Zamfara da Katsina sun ce a shirye suke su dafa wa gwamnatin tarayya domin taimaka mata wajen hako man fetur a yankin Arewacin Najeriya.
Gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ne ya bayyana hakan Alhamis din da tagabata a jihar Sokoto, inda ya ce gwamnatin sa za ta taimakawa gwamnatin tarayya wajen ganin an hako man fetur a arewacin kasar musamman ma a jihar sa ta Sokoto.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin taron masu fasahar kimiyya kan yadda za’a hako man fetur a tafkin Sokoto da ke gudana a jama’ar Usumanu Danfodiyo da ke Sokoto.
Asusun bunkasa bangaren man fetur ne suka shirya taron da hadin gwiwar gwamnatin jihar Sokoto da kuma jami’ar ta Usmanu Danfodiyo domin bunkasa binciken Masana da kuma musayar fasaha kan yadda Yakamata a tono man a tafkin na Sokoto.
Waziri Tambuwal ya ce akokarin sa na ganin an hako mai a jihar, gwamnatin jihar ta nemi wani Kamfanin kasar China wanda zai yi binciken wurin ya kuma tabbatar da adadin man da ke wurin wanda shi zai bada damar hakoshi.