Kiwon Lafiya
Wasu jami’an yan sanda 3 sun mutu sakamakon harin yan bindiga da ya rutsa da su a jihar Nassarawa
Rundunar ‘yan sandan jihar Nassarawa ta tabbatar da mutuwar wasu jami’an ta uku, sakamakon harin wasu ‘yan bindiga da ya rutsa da su a kauyen Maraban-Udege da ke yankin karamar hukumar Nassarawa.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar a jihar Nassarawa ASP. Sama’ila Usman ne ya bayyana hakan yau a Lafiya lokacin da yake ganawa da manema labarai, inda yace al’amarin ya rutsa da jami’an ‘yan sandan ne lokacin da suke kokarin sasanta rikicin da ya kunno kai tsakanin manoman Agatu da kuma wasu makiyaya.
Kakakin rundunar ‘yan sandan na jihar Nassarawa ya kuma ce yanzu haka rundunar ta baza jami’an ta karkashin jagorancin Kwamishinan ‘yan sandan jihar domin binciko wadanda ke da hannu a kisan jami’an ta.
Duk da cewa bai bayyana sunayen jami’an ‘yan sandan da suka rasa rayukan nasu ba, sai dai yace akwai mai mukamin sufeto da sajan da kuma kofur, tare da cewa yanzu haka an mika su dakin ajiye gawa da ke asibitin Lafiya.
Rahotanni sun ce jihar ta Nassarawa da makociyar ta jihar Benue na fama da rikicin manoma da makiyaya, lamarin da ke cigaba da jawo asarar rayuka da dama, inda Masana ke ganin hakan ka iya jawo matsalar yunwa sakamakon kalubalen noma abinci da ke barazanar tunkarar manoma saboda matsalar makiyaya.