Kiwon Lafiya
Wasu yan bindiga sun kashe ma’ajin direbobin hanya ta kasa reshen Jibowu-yaba
Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne, sun kashe ma’ajin kungiyar direbobin hanya ta kasa reshen Jibowu-Yaba Alowonle Asekun wata makaranta dake Ikorodu dake jihar Lagos.
Rahotanni sun bayyana cewar, ma’ajin kungiyar na kan hanyar sa ta zuwa wata makaranta a kan hanyar Ajasa-Lamberu, yayin da ‘yan bindigar suka harbe shi a ranar Juma’ar da ya gabata.
Wani ganau ya bayyana cewar, kashe ma’ajin kungiyar direbobin ya haifar da fargaba a zukantan al’ummar yankin Jibowu da kuma Fadeyi.
Haka zalika wani ganau Akeem Adepoju ya ce ‘yan bindigar sun harbi Asekun har sau 3 kafin mutuwar sa.