Labarai
Wasu ‘yan Najeriya sun kamu da cutar COVID-19 a kasar Sin
Wasu ‘yan Najeriya 7 sun kamu da cutar Coronavirus a China, bayan da aka yi musu gwaji suna dauke da cutar, ya yin da suka ci abinci da wasu ‘yan kasar China a gidan abinci tare.
Wannan na dauke cikin jaridar Daily Mail ta wallafa a shafin ta na Internet cewa hakan na zuwa ne bayan da kasar ta Sin ta ce kamuwa da cutar da ‘yan Najeriyar suka yi da cutar na nuna cewar an sake samun bullar cutar a kasar.
Hakan na zuwa ne bayan da hukumomin gudancin yankin Guangzhou ke binciken wasu mutane da ake ganin suke yada cutar mai sauran kisa.
Kwamishinan lafiya na yankin Guangzhou ya ruwaito cewar, mamallakin gidan abinci da ‘yar sa guda da kuma wani ma’aikaci bayan an guda su suna dauke da cutar ta COVID-19.
You must be logged in to post a comment Login