Labarai
Wata babbar kotu a Abuja ta bukaci kame tare da bincikar Hajiya Hafsat Umar Ganduje
Wata babbar kotun birnin tarayya Abuja da ke zama a Maitama ta bukaci a gaggauta saurarar karar da aka shigar gabanta na tilsatawa hukumar EFCC ta kama tare da bincikar mai dakin Gwamnan kano Abdullahi Umar Ganude, wato Hajiya hafsat Umar Ganduje bisa zarginta da taka muhimmiyar rawa kan zargin cin hancin da ake yiwa Gwamnan Kanon.
Haka kuma kotun karkashin mai shari’a Yusuf Halilu ta bukaci hukumar EFCC da gwamnatin jihar Kano da jam’iyyar APC su yi mata bayanin hujjar da ta sa ba za a kwace kadarorin da Gwamnan da matar sa suka mallaka ba na wucin gadi har a kammala binciken
Haka kuma kotun dai ta bukaci jam’iyyar APC da ta yi bayanin dalilan da suka sanya taki bada umarnin sauya sunan Gwamnan a matsayin dan takarar ta a zaben mai zuwa ta kuma musanyashi da wani mutumin na daban domin kaucewa rudani.
Cikin karar dai da wasu kungiyoyi masu zaman kansu suka shigar gaban kotun sun bukaci kotun ta tilstawa hukumar EFCC ta kwace dukkanin kadarorin da Gwamna Ganduje da matar sa suka mallaka har sai abinda kotu tayi hukun ci a kai.
Tun a kwanakin baya ne dai jaridar Daily Nigeria ta fito da wasu faifan bidiyo da ake zargin na nuna hoton Gwamnan Ganduje na karbar na goro a hannun yan kwangila da ya kai dala miliyan biyar.