Labarai
WHO zata binciki China kan yadda aka samu asalin cutar Corona
Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce, kungiyoyin masana kimiyyar lafiya dake karkashin hukumar guda goma ne za su ziyarci kasar China a ranar Alhamis mai zuwa don bincika yadda cutar corona ta samu Asali duk da kokarin da Beijing ke yi na kokarin dakile binciken.
Hakan na cikin wata sanarwar da shugaban hukumar lafiya ta duniya Tedros Adhanom ya fitar a yau Litinin yana mai cewa duk da kasar China ta dakatar da tawagar shiga kasar hakan ba zai dakile kudirin tawagar kungiyoyin ba.
A don haka za su killace kan su na tsawon makwanni biyu kafin shiga kasar.
Ya ce, yanzu haka fiye da shekara guda ke nan da bullar cutar a duniya, a don haka WHO za ta gudanar da hadin gwiwar bincike don gano asalin cutar ta corona tare da masanan na kasar China.
Tedros ya kuma ce , Kwararrun na WHO za su kebe kansu na tsawon makonni biyu lokacin da suka isa kasar ta China; amma ana sa ran daga baya za su ziyarci Wuhan garin da aka fara gano mummunar cutar a karshen 2019.
Beijing dai ta gamu da suka daga kasashen duniya kan rashin nuna gaskiya a yayin barkewar Annobar karon farko, ko da yake a cikin gida gwamnatin kasar ta yaba da yadda take kula da cutar tare da dakile duk wani suka da ake mata.
You must be logged in to post a comment Login