Labaran Wasanni
World Cup 2022: Qatar za ta kaddamar da filayen wasanni 6 gabanin gasar
Shekara guda kafin fara gasar cin kofin Duniya ta shekarar 2022 da za’a gudanar a kasar Qatar.
Hukumar kwallon kafa ta kasar za ta kaddamar da filayen wasanni 6 a watan Oktobar 2021 kafin fara gasar.
Bude filayen wasannin zai gudana a ranar 22 ga watan Oktobar da wasan karshe na gasar (Amir Cup) na kasar.
Qatar 2022: Kasar Masar ta sallami mai horar da ‘yan wasan ta
Filayen wasannin da suka hada da na Al-Thumama da na Khalifa International, sai kuma Al Janoub da Education City da Ahmad Bin Ali da kuma na Al-Bayt, filayen da tuni suka zama cikin shiri gabannin gasar ta shekarar 2022.
Kungiyoyi biyu da suke buga gasar a kasar ta Qatar da su ka hada da Al-Sadd da tsohon dan wasan Barcelona da kasar Sipaniya Xavi Hernandez ke jagoranta da kuma kungiyar Al-Rayyan da dan kasar Faransa Laurent Blanc ke jagoranta sune za su buga wasan na karshe a gasar ta Amir Cup.
Filin wasa mai daukar mutane dubu 40,000 na Al-Thumama zai karbi bakuncin wasannin gasar har zuwa wasan dab dana kusa dana karshe.
Gasar cin kofin duniya a Qatar dai za ta gudana daga ranar 21 ga Nuwamba zuwa 18 ga Disambar shekarar 2022.
You must be logged in to post a comment Login