Labaran Wasanni
World Cup Qualify 2022: Najeriya ta doke kasar Cape Verde da ci 2-1
Kungiyar kwallon kafa ta Kasa Super Eagles ta doke kasar Cape Verde da ci 2-1 a wasan neman tikitin buga kofin Duniya da za a gudanar a shekarar 2022 a kasar Qatar.
Wasan da aka buga a babban filin wasa na Estádio Municipal Adérito Sena, dake yankin Mindelo a kasar ta Cape Verde.
Nasarar da Najeriya ta samu a yau Talata 7 ga Satumbar shekarar 2021 ya bata damar darewa zuwa mataki na 1 da maki 6 a rukunin da take na C.
Najeriya dai ta warware kwallon da aka zura mata ta hannun dan wasan gaban ta dake wasa a kungiyar kwallon kafar Napoli dake kasar Italiya Victor Osimhen, bayan samun tai mako daga hannun dan wasa Jamilu Collins a minti na 30.
Tunda da fari dai dan wasan kasar Cape Verde Dylain Tavares ne ya zurawa Najeriya kwallo a minti na 19 da fara wasan.
Sai dai mintina kadan a kammala wasan Kenny Santos ya zura kwallo a ragar kasarsa wato Own goal a minti na 77 da hakan ya bawa Najeriya nasara.
Da sakamakon ne Najeriya ke a mataki na 1 a rukinin da take na C da maki 6, inda Liberia ke biye mata a matsayin ta 2 da maki 3 sai kasar Cape Verde da Afrika ta tsakiya dake da maki 1 kowannan su.
You must be logged in to post a comment Login