Jigawa
Yaƙi da bahaya a sarari: An hana ɗaura aure sai da shaidar haƙa masai a Jigawa
Majalisar ƙaramar hukumar Ɓaɓura a jihar Jigawa ta zartar da dokar hana ɗaura Aure har sai an gabatar da shaidar haƙa Masai a gida bisa tsari.
Shugaban ƙaramar hukumar ɓaɓura Alhaji Lawan Isma’il Kanya ne ya bayyana hakan a zantawarsa da Freedom Radio.
Kanya ya ce, maƙasudin samar da dokar shi ne a daƙile ɗabi’ar bahaya a sarari da kuma gyaran tarbiyyar ƙananan yara”.
“mun samu ƙorafi kan yadda ake samun ɗabi’ar yin bahaya a fili kuma irin wannan yana janyo yawaitar fyaɗe”.
Ya kuma ce, tuni majalisa ta sanya hannu kan dokar wadda kuma an rarraba ta ga masu ruwa da tsaki na ƙaramar hukumar.
Sai dai ya ce, dokar zata tabbatar da an hana ɗauka aure gabanin gabatar da shaidar samar da banɗaki a muhalli kuma za a fara aiwatar da dokar makwanni biyu masu zuwa.
You must be logged in to post a comment Login