Kiwon Lafiya
Ya kamata mutane su rika bin hanyoyin kare kai daga kamuwa da cutukan zafi-Dr Sabitu Shu’aibu
Wani kwararren likita a sashen kiwon lafiya na Asibitin koyarwa na Aminu Kano da ke nan Kano, Dakta Sabitu Shu’aibu, ya ce duba da yadda yanayin zafi ke shigowa a halin yanzu, ya kamata mutane su rika bin hanyoyin da za su kare su daga kamuwa da cututtukan da yanayin zafin ke haddasawa.
Dakta Sabitu Shu’aibu, ya bayyana hakan ne a jiya ta cikin shirin Mu Leka Mu Gano na musamman na nan tashar Freedom Rediyo, wanda ya maida hankali kan sauyin yanayi da ake fuskanta a halin yanzu.
Ya ce ya kamata al’umma su lazimci yawan shan ruwa tare da bin hanyoyin da za su kare kansu daga kamuwa da cutukan zafi, musamman ma cutar sankarau da dangoginta.
Haka zalika ya kara da cewa, idan an samu wanda ya kamu da wata daga cikin cututtukan da suka danganci zafi, kamata ya yi a fara bin hanyoyin da za su sanyaya jiki gabanin zuwa asibiti, don hakan na saukaka ta’azzarar cututtukan.
Likitan ya kuma ce rashin tsaftace muhalli musamman ma a lokacin damuna, hakan na daga cikin hanyoyin da ke janyo kamuwa da cutuka masu yaduwa a tsakanin al’umma.