Labaran Wasanni
Ya kamata ‘yan jarida su samu yancin kawo rahoton wasanni ba tare da fargaba ba – CAF
Hukumar kwallon kafa ta Afirka, CAF ta ce da akwai bukatar kafafen yada labarai su samu yancin kawo rahotannin wasanni a nahiyar ba tare da fargaba ba.
A wata sanarwa da daraktan sadarwa na hukumar, Alexandre Siewe ya fitar, ya ce wajibine hukumomin kwallon kafa dake nahiyar ta Afirka su yi duk mai yiwuwa wajen tabbatar da samun yancin kafafen yada labaran.
“Dole ne a mutunta wuraren da kafafen yada labarai ke gudanar da ayyukan su, tare da kuma kare ‘yan jaridun da ke daukar labarai,” in ji Siewe.
Jami’in hukumar ta CAF ya bayyana cewa hukumar ta lura da abin da ya faru a ranar Laraba 23 ga watan Yunin 2021 yayin wasan Asante Kotoko da ta fafata da Karela United a gasar Firimiyar kasar.
Yayin wasan, magoya baya sun shiga wuraren da kafafen yada labarai ke gudanar da aikin su, lamarin da ya haddasa rikici da wakilin kafafen yada labarai, Andy Abraham Mantey.
You must be logged in to post a comment Login